Kayayyakin Sinadarai - Chemical products

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Kayayyakin Sinadarai (Chemical Products)


Gabatarwa

Abin da ake nufi da kayayyakin sinadarai a nan shi ne kayayyakin amfanin yau-da-gobe da ake yi daga sinadarai (chemical) waɗanda ka iya zama abinci, sha ko kuma waninsu.

Kalli Wannan Bidiyon Domin Ƙarin Haske

Mai karatu, na san bakin gwargwado idan zan tambaye ka cewa waɗanne kayayyaki ne ka sani a cikin ɗakin da ka ke ko ofishin da ka ke waɗanda kemistiri ke samarwa, ba za ka rasa abin faɗa ba. Tana ma iya yiwuwa yanzu a kusa da kai ba za a rasa abin ci ko sha ko kuma turaren saka ɗaki ƙamshi ba ko kuma ma yanzu haka da turare a jikinka ko rigarka da sauran abubuwan da suka yi kama da wannan. To ka sani cewa mafiya yawan waɗannan kayayyaki daga sinadarai (chemicals) aka samar da su. Kuma cewa, matuƙar ba a yi amfani da su bisa hanyar da ta dace ba, sukan jirkice su koma guba.

A wannan darasin na yau, za mu zayyano sunayen wasu daga cikin waɗannan kayayyaki, sannan kuma mu faɗi irin illar da suke yi wa lafiyar ɗan’adam da kuma hanyoyin kaucewa wannan illa. Ga su kamar haka:

1. Turare: dukkan nau’ukan turarrukan zamani da ake amfani da su kamawa tun daga na jiki, tufafi har zuwa na ɗaki, da sinadarai ake harhaɗa su. Abin nufi, chemical products ne su.
2. Sinadaran kashe ƙwari (insecticide): Sinadaran da muke amfani da su a gidaje da sauran guraren walwalarmu a matsayin kayayyakin kare lafiya, samammu ne su daga sinadarai; wato chemical products ne su. Duk da cewa, sukan karkashe mana ƙwari masu cutarwa kamar irin su sauro, to su ma suna cutarwa matuƙar dai ba a yi amfani da su bisa ƙa’ida ba.
3. Sabulan wanka da na wanki (soap and detergents): Sinadarai ne da ke taimaka mana wajen tsaftace jiki, muhalli, tufafi, mazubin abinci da sauran su. A wannan ayarin akwai sinadarai irin su detergents, soaps, bleach da sauran su. Da yawa daga cikin su sukan haifar da illa matuƙar aka kuskurewa amfani da su.
4. Allin rubutu (chalk): Alli da muke rubutu da shi a makaranta. Shi ma chemical product ne. Rashin bin hanyar da ta dace wajen yin amfani da shi kan haifar da illa ga lafiya.
5. Alƙalami (pen): Alƙaluman rubutu da suka haɗa da biro da sauran su, dukkansu samammu ne daga sinadarai. Suna da amfani da kuma akasin haka.
6. Sukari (sugar): Sukarin da muke sha a cikin abubuwan sha kamar irin su fura, kunu, koko da sauran su, duk samammu ne daga sinadarai. Akwai buƙatar taka tsantsan wajen amfani da su.
7. Lemuka (juice): Lemukan kwalba, gwangwani, roba, takarda da sauran su, mafiya yawan su da sinadarai ake harhaɗa su. Bayan an kammala shan su kuma sukan bar baya da ƙura a wasu lokutan.
8. Magunguna (medicine): Magunguna da muke sha domin warkar da cututtuka da suka haɗa da na ruwa, ƙwayoyi, allurai, na shaƙa, shafawa da sauran su, samammu ne daga sinadarai. Rashin bin ƙa’ida wajen amfani da su kan haifar da cutar da ta fi wadda aka je neman maganin ta illa. A wasu lokutan ma sukan kai ga rasa rai ɗungurumgum ko kuma wani sashen jiki.
9. Albarkantu mai (oil and gas): Albarkatun mai da muke amfani da su a ko’ina a matsayin makamashi kamawa tun daga iskar gas da muke girki da ita har zuwa man da muke zubawa a injina da ababen hawa, samammu ne daga sinadarai. Mafi ƙaranci illar da suke haifarwa ita ce shaƙar hayaƙin da suke fitarwa ba bisa ƙa’ida ba.
10. Gishiri (salt): Gishirin da ake miya da shi yana daga cikin haɗe-haɗen sinadarai. Baya rasa illa idan aka kuskure.

Illon da Kayayyakin Sidarai ke Haifarwa
Illolin da sinadarai ke haifarwa suna da yawa, akwai manya kuma da ƙanana. Suna kuma iya faruwa a gida, wajen aiki ko kuma wajen sana’a. Kaɗan daga cikin su akwai:

  1. Guba (poisoning).
  2. Tashin zuciya da amai (nausea and vomiting).
  3. Ciwon kai (headache).
  4. Ƙurajen fata (skin rashes).
  5. Ƙuna (chemical burns).
  6. Matsalar haihuwa (birth defects).
  7. Tangarɗar huhu, hanta da zuciya (disorders of the lung, kidney or liver).
  8. Tangarɗar tsarin saƙonni (nervous system disorders).
  9. Toshewar hanci (blockage of nose).
  10. Matsalar nimfashi (respiratory problems).

Hanyoyin Kariya

  1. Saka kayayyakin kariya a lokacin amfani da sinadarai masu guba a lokutan aiki kamar irin su takunkumi, safar hannu, takalmin roba da sauran su.
  2. Samar da ingantaccen yanayi mai iska.
  3. Kiyayye sharruɗan shan magani bisa shawarar likita.
  4. Karanta takardar bayanin da ke jikin kayan amfani.
  5. Bin umarnin kamfanin da suka samar da kayan amfani a lokacin amfani.
  6. Kasancewa cikin muhalli mai tsafta da kuma wadatacciyar iskar shaƙa mai tsafta.
  7. Tsaftacce muhalli.
  8. Wurgar da mazubin kayayyakin da aka yi su domin amfanin lokaci guda (disposable).
  9. A nisanci gauraya sinadaran waki kala biyu a lokaci guda musamman waɗanda ke ɗauke da sinadaran amoniya (ammonia) da kulorin (chlorine) kamar bilic (bleach) da sauran su.
  10. A riƙa yin amfani da safar hannu ta roba a yayin amfani da sinadaran wanki.
  11. A nisanci yin wanka da sinadaran da aka yi domin wanki ko kuma shafa sinadari sutura a fatar jiki.

Manazarta:


ACS Chemistry for Life (2020). Chemistry Careers. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.acs.org/content/acs/en/careers/college-to-career/chemistry-careers.html

AGCAS (2020). Chemistry. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.prospects.ac.uk/careers-advice/what-can-i-do-with-my-degree/chemistry

AGCAS (2020). Nuclear engineer. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.prospects.ac.uk/job-profiles/nuclear-engineer

Better Health (2017). Workplace safety - hazardous substances. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.betterhealth.vic.gov.au/health/healthyliving/workplace-safety-hazardous-substances

Cleveland Clinic (2018). Household Chemical Products and Their Health Risk An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://my.cleɓelandclinic.org/health/articles/11397-household-chemical-products-and-their-health-risk

Mendeley (2018). Top Ten Chemistry Jobs. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.mendeley.com/careers/article/top-10-chemistry-jobs/

Moore J.T (2020). Ten Great Careers in Chemistry. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.dummies.com/education/science/chemistry/ten-great-careers-in-chemistry

Tucker L. (2019). What Can You Do With a Chemistry Degree? An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.topuniversities.com/student-info/careers-advice/what-can-you-do-chemistry-degree

United States Department of Labor (2020). Chemical Hazards and Toɗic Substances. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.osha.gov/SLTC/hazardoustoxicsubstances/


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub